HAUSA DA NAHAWUNTA Daga Bello Muhammad Danyaya

HAUSA DA NAHAWUNTA

  • Daga Bello Muhammad Danyaya
       Ban san wani abu ba, da zan fada wanda ba a fada ba, game da Nahawun Hausa, sai dai Hausawa sun ce “Mai rai bai rasa motsi”. Saboda haka, zan dan ce wani abu game da wannan Nahawu na Hausa.
        Ina sane da cewa, manyan malamai sun yi bayani mai yawa game da wannan sha'ani na Nahawun Hausa, Kamar su M.K.M Galadanci, Dauda Bagari, Hambali Jinju, Ahmadu Bello Zariya da kuma Sani Zariya. Tabbas wadannan malamai sun yi bayani mai yawa game da Nahawun Hausa. Kuma har yanzu kokarinsu ne manazarta da malamai da dalibai ke biye.
Ni ma kaina kokarin wadannan malamai ne na tsaya na duba, sai na yi wani abu mai kama da abin da Hausawa kan ce, “An yi tsintuwar guru cikin sudi”. Watau na gano wasu abubuwa masu yawa a cikin nazarce-nazarcensu.
Idan mutum ya duba zai iya ganin karantarwata ta dan bambanta da karantarwar magabata. Wannan ba abin mamaki ba ne, tunda sha'anin ilimi haka ya gada. Kuma ma an ce “Da Na gaba akan gane zurfin ruwa”.
MA'ANAR NAHAWU
        A nawa ra'ayi, Nahawu shi ne ilimin da ke nazari kan ka'idojin gina jimla mai ma'ana, tare da da bayyana rukunin kowace kalma da ke Jimla, hade da fayyace matsayin kowace kalma da ke jimla, hade da kulawa da ingancin wasalin karshen kowace kalma da ke jimla.
        Idan an kula da wannan ma'ana da na bayar ta Nahawu, za a ga a wurina Nahawu ya tsaya ne kacokam, kan nazarin abubawa hudu:
Jimla mai ma'ana
Rukunin kalma
Matsayin kalma
Ingancin wasalin karshen kalma
JIMLA MAI MA'ANA
        Jimla dai ita ce cikakkiyar magana mai gamsarwa.
        To kafin jimla ta kasance mai gamsarwa, sai ta kasance a tsare, kamar yadda Bahaushe kan tsara ta. Misali:
Audu dalibi ne
Audu ne dalibi
Dalibi ne Audu
Bahaushe haka yakan tsara kalmomi, idan yana son nuna dalibtakar Audu. A nan ilimin Nahawu zai tabbatar da cewa wadannan jimloli sun tsaru daidai da yadda Bahaushe kan tsara. To amma idan aka ce:
Ne dalibi Audu 
Ne Audu dalibi
A nan Nahawu zai duba ya ce, wadannan jimloli ba su yi ba, saboda Bahaushe bai cewa haka idan ya tashi tsara jimla kan dalibtakar Audu.
        Wannan shi ne ake nufi da cewa, Nahawu na nazari kan k'idar gina jimla mai ma'ana.
RUKUNIN KALMA
        Rukuni kalma ce ta Larabci. A Hausance tana da ma'anoni, daga ciki akwai NAU'I. Watau idan aka ce abubuwa suna rukuni daya, ana nufin nau'insu daya, game da abin da ya hada su. To a nan ma, idan na ce rukunin kalma ina nufin nau'inta. Misali:
    KALMA        RUKUNI
1. Mutum        Suna
2. Makaho       Sifantau
3. Karfi           Sifa
4. Duba          Aiki
5. Watau        Harafi
        Idan an kula, an sami rukunai da ban-da ban. Watau a cikin kalmomin Hausa, akwai wadanda ke rukunin suna, sifantau, sifa, aiki da harafi.
        To, ilimin Nahawu hakkinsa ne ya yi wa mai karatu bayanin wadannan rukunai na kalmomi.
MATSAYIN KALMA
        Kamar yadda Nahawu ke bincike kan rukunin kalmomi, haka kuma yana bincike kan matsayin kalmomi a jimla. Misali, Nahuwu ne ke gaya wa mai karatu, wannan kalma matsayinta ma'aikaci a jimla. Wannan kuwa ita ce mafadar aiki, waccan kuwa bayanau ce.
INGANCIN WASALIN KARSHIN KALMA
         Ingancin karshen kalma yana nufin sa wasali a karshenta kamar yadda ya kamata. Misali:
Musa Audu Ya mara
Musa Audu ya maro
Musa Audu Ya mare
A duba wasalin karshen kalmar (MARA) a jimla ta (1), za a ga an saka wasalin (a). A jimla ta (2), kalmar (MARO), tana da wasalin (o), a karshenta. A jimla ta (3), kalmar (MARE) tana na da wasalin (e) a karshenta. Wannan yana nufin, idan Bahaushe zai ya jinkirtar da kalmar aiki ta MARI a bayan ma'aikaci to zai yi amfani ne da dayan wasula uku a wannan kalma. Wadannan wasula su ne: a, o, da e. Sake duba wannan jimla:
Musa ya mari Audu
Kula da wasalin kalmar (MARI), za ka ga tana da wasalin (i). Wannan yana nufin, idan Bahaushe ya gabatar da ma'aikaci a kan aiki na kalmar MARI, to zai yi amfani ne da wasalin (i) kadai a karshen kalmar.
To, yanzu duba wadannan jimloli:
Musa  Audu ya maru
Musa Audu Ya mari
Musa Ya maru Audu
Wadannan jimloli gaba-daya ba su yi ba, saboda an sami rashin ingancin wasalin karshen wasu kalmomi a ciki. Duk wannan akan gane shi ta hanyar ilimin Nahawu.
        A takaice dai, mun gano Nahawu dai na binciki ne kan abubuwa hudu: Jimla mai ma'ana, rukunin kalma, matsayin kalma da ingancin wasalin karshen kalma.
         Bari mu kwana a nan, a mujalla ta gaba za mu dora a inda muka kwana.

No comments:

Post a Comment

makamancin wannan

ILIMIN FURUCI

ILMIN FURUCI   Da farko dai kafin mu shiga gundarin batun namu yana da kyau musan maye ma'anar furuci bisa ƙarmar fahimtar mu. FURUCI...