Thursday 12 January 2017

ILIMIN FURUCI

ILMIN FURUCI
  Da farko dai kafin mu shiga gundarin batun namu yana da kyau musan maye ma'anar furuci bisa ƙarmar fahimtar mu.

FURUCI: zamu iya cewa furuci shine aiwatar da sautin magana a baki.

ILMIN FURUCI: wannan ilmi na furuci, kamar yadda sunan ya nuna, ya danganci bayani ne na yadda ake furta sutin magana, wato baƙo ko wasali na harshe.ƙwararre a wannan fage na ilmi an masa laƙabi da masanin furuci. akwai hanyoyi iku fitattu da ake bi wajen bayyana wannan sauti. za a iya bin hanyar da sutin kansa ke fita a baki, wato fannin furta sauti. za aiya bin hanyar ji da kunne , game da yadda sautin yake fita, wato fannin jin sauti. haka kuma, za aiya bin hanyar nazarin kamannin sautin fitatt, wato fannin kamannin sauti. amma a duk hanyoyin nan uku da ake bi wajen bayyana sauti, hanya ta farko tafi, bisa wasu dalilai.na farko dai tafi saukin kashe kudi domin ba abuƙatar wasu naurori na musamman na biyu kuma, wannan hanya ta fi sauƙin fahimta. sarƙaƙiyarta bata kai ta sauran biyun ba ko kaɗan.saboda haka wannan hanya dai za mu bi mu bayyan sautukan hausa a wannan shafi.

makamancin wannan

ILIMIN FURUCI

ILMIN FURUCI   Da farko dai kafin mu shiga gundarin batun namu yana da kyau musan maye ma'anar furuci bisa ƙarmar fahimtar mu. FURUCI...